27 Afirilu 2021 - 12:36
Salami: Iran Za Ta Mayar Da Martani Mai Tsanani Akan Duk Wani Gigin Isra'ila

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran manjo janar Hussain Salami wanda tashar talabijin din ‘almayadden’ ta yi hira da shi, ya yi Magana akan abinda yake faruwa a yankin Gaza, yana mai cewa; Duk wata wuta da ‘yan sahayoniyar za su kunna, za ta koma ne akansu.”

ABNA24 : Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma ce; A cikin kwanakin bayan nan, duniyar ta ga yadda sharrin da ‘yan sahayoniyar su ka bude ya zamar musu kaikayi koma kan mashekiya, don haka jamhuriyar musulunci ta Iran za ta mayar da martani mai karfin gaske akan duk wani gigin na ‘yan sahayoniya.

Kwanaki kadan da su ka gabata kafafen watsa labarun HKI sun ce an ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi a yankin “ Bi’iri-Saba’a” da kuma a tsakiyar Palasdinu da ke karkashin mamaya.

342/